Shugaba Biya Ya Jagoranci Zaman Majalisar Zartarwa Na Farko Tun 2015
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya a jiya Alhamis ya jagoranci taron majalisar zartarwar kasar a karon farkon tun shekara ta 2015 inda ya bukaci 'yan majalisar da su yi kokari wajen karfafa tattalin arzikin kasar da kuma ba wa jami'an tsaron umurnin su murkushe 'yan awaren kasar.
Rahotanni daga kasar Kamarun sun ce shugaba Biyan wanda ba kasafai yake halartar zaman majalisar zartarwar ba, a jiyan ya halarta inda daga cikin batutuwan da ya fi ba su muhimman a yayin tattaunawar shi ne batun 'yan awaren yankunan da suke magana da harshen Turancin Ingilishi inda ya ba da umurnin a dauki matakan ba sani ba sabo a kansu.
Shugaba Biyan wanda yake mulkin kasar Kamarun tun shekarar 1982 ya ce daukar matakin sojan shi ne abin da ya fi dacewa kan 'yan awaren wadanda suke ci gaba da kokawa dangane da irin wariyar da yake nuna musu, inda a shekarar bara 2017 suka shelanta kafa kasarsu da suka kira Ambazonia.
Rahotanni dai sun ce a mafi yawan lokuta ministocin gwamnatin Kamarun ba sa samun damar ganawa da shugaba Biya din sai dai ko a filin jirgi ko kuma a cikin jirgin sama a yayin da yake balaguro zuwa kasashen waje wanda ya zamanto ruwan dare dama duniya a wajensa.