Martanin MDD Kan Sace Alkarin Kotun Soja A Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i29264-martanin_mdd_kan_sace_alkarin_kotun_soja_a_libiya
MDD ta bukaci a dauki matakin da ya dace na kare lafiyar alkalin kotun soja da aka yi awan gaba da shi a kasar Libiya.
(last modified 2018-08-22T11:31:35+00:00 )
Mar 21, 2018 06:30 UTC
  • Martanin MDD Kan Sace Alkarin Kotun Soja A Libiya

MDD ta bukaci a dauki matakin da ya dace na kare lafiyar alkalin kotun soja da aka yi awan gaba da shi a kasar Libiya.

Cikin wata sanarwa da suka fitar, Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar Libiya sun nuna damuwarsa kan sace  Massoud Erhuma babban alkalin kotun soja na kasar da 'yan bindiga suka yi awan gaba da shi , tare da bayyana cewa wannan babban cikas ne ga Hukumar kasar ta Libiya.

A ranar 15 ga watan Maris din da muke ciki ne, wasu 'yan bindiga suka yi awan gaba da Massoud Erhuma babban alkalin kotun sojan kasar a kofar gidansa dake birnin Tripoli babban birnin kasar, kuma ya zuwa babu wani gungu ko kungiya da ta dauki alhakin sake shi.

A nasa bangare, kwamitin kare hakin bil-adama na kasar Libiya ya bayana lamarin da rashin mutunta magabatan shari'a a kasar, inda ya bukci a gaggauta gudanar da bincike domin hukunta wadanda suka aikata wannan laifi.