Libya: Da'esh Ta Dauki Alhakin Kai Hari A gabacin Kasar
(last modified Fri, 30 Mar 2018 19:10:27 GMT )
Mar 30, 2018 19:10 UTC
  • Libya: Da'esh Ta Dauki Alhakin Kai Hari A gabacin Kasar

An kai hari ne wani wurin binciken soja da ge garin Ajdabiya agabacin kasar ta Libya

Kamfanin dillancin labarun faransa ya nakalto cewa; A yau juma'a ne kungiyar ta Da'esh ta sanar da cewa ita ce ta tashi wata mota mai bama-bamai a wurin bincike na jami'an tsaro da ke garin Ajdabiya a gabacin kasar Libya.

Kungiyar ta Da'esh ta ce wanda ya kai harin da motar shi ne wani mutum mai suna Kudamah al-Sa'ih.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 8 da suka hada soja da fararen hula, yayin da wasu mutane 8 su ka jikkata.

Wannan shi ne karo na biyu da aka kai harin ta'addanci a cikin garin Ajdabiya a cikin wata guda.

Harin 9 ga watan Maris ya kashe mutane uku da kuma jikkata wasu dama. Shi ma kungiyar ta Da'esh ce ta dauki alhakin kai shi.

Libya tana cikin matsalar tsaro tun a 2011 da aka kifar da gwamnatin Mu'ammar Kaddafi.