Kamaru : An Ceto 'Yan Kasashen Waje 12 Da Ake Garkuwa Da Su
Hukumomin Kamaru sun ce sojojin kasar sunyi nasara ceto wasu 'yan kasashen waje 12 da akayi garkuwa dasu a yankin masu magana da turancin Ingilishi.
Hukumomi a kasar Kamaru sun ce an sako wasu 'yan kasashen Turai 12 da aka yi garkuwa da su a yankin yammacin kasar inda masu amfani da harshen turancin Ingilishi ke neman ballewa don kafa kasar Ambazoniya.
Daga cikin mutanen 12 da aka sako da suka je yawon buda ido a wajen, bakwai daga cikinsu 'yan kasar Switzerland ne, sannan sauran biyar kuma 'yan kasar Italiya ne
Dakarun kasar Kamarun sun ce sun kubutar da mutanan ne daga hannun 'yan ta'addan yankin kudu maso yammacin kasar ne, kamar yadda ministan sadarwa Issa Tchiroma Bakary, ya tabbatar.
A bangare guda kuma wasu bayanan sun tabbatar da mutuwar wasu dakarun Kamarun su biyar a wani harin da 'yan bindiga suka kaddamara s yankin arewa mai nisa. Sai dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin harin.