Somaliya Ta Dakatar Da Shirin UAE Na Horar Da Sojojin Kasar
Kasar Somaliya ta dakatar da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) daga shirin da take aiwatarwa a kasar na ba da horo ga daruruwan sojojin kasar a wata alama da ke nuni da irin tsamin da alakar da ke tsakanin kasashen biyu ta ke ci gaba da yi.
Ministan tsaron kasar Somaliya Mohamed Mursal Abdirahman ne ya shaida hakan a wata hira da yayi da Kamfanin dillancin labaran kasar Somaliyan SONNA a yau din nan Laraba inda ya ce gwamnatin kasar za ta dauki nauyin biya da kuma horar da sojojin.
Tun a shekara ta 2014 ne UAE ta dauki nauyin horar da daruruwan dakarun kasar Somaliyan a shirin kungiyar Tarayyar Afirka na fada da kungiyoyin ta'addancin da suke gudanar da ayyukansu a kasar Somaliyan da kuma karfafa gwamnatin kasar da take samun goyon bayan kasashen duniya.
Alaka tsakanin Somaliya da UAE din dai ta fara tsami ne sakamakon rikicin da ya kunno kai tsakanin kasar Qatar da Saudiyya wanda gwamnatin Somaliyan ta ki goyon bayan kowane bangare.
A ranar Lahadin da ta wuce ma jami'an tsaron kasar Somaliyan suka kwace wasu kudade da suka kai dala miliyan 9.6 daga wani jirgin saman UAE da ya sauka a birnin Mogadishu suna cewa sai sun gudanar da bincike kan ina za a kai wadannan kudaden, wanda gwamnatin UAE din tace wai za ta yi amfani da shi ne wajen biyan sojojin albashi.