Ana Ci Gaba Jajanta Wa Aljeriya, Bayan Hatsarin Jirgin Sama
Duniya na ci gama da aike wa da sakon ta'aziyya ga gwamnatin Aljeriya da al'ummarta, biyo bayan mumunnan hatsarin jirgin saman soji da ya yi ajalin mutum 257
Jamhuriya musulinci ta Iran, ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajenta, Bahram Qassemi ta aike da sakon ta'aziyya ga iyalen wadanda hadarin ya rusa dasu.
Ita ma kasar Masar ta aike da sako makamancin wannan, inda ministan harkokin wajen kasar, ya taya al'ummar Aljeriya juyayi game da halin da ake ciki.
A nasa bangare kuwa babban sakataren kungiyar kasashen larabawa, Ahmed Aboul-Gheit, shi ma ya aike da sakon juyayi ga al'umma da kuma gwamnatin kasar ta Aljeriya.
A kalla mutane 257 ne galibi sojoji da iyalensu suka rasa rayukansu a hadarin jirgin saman daukan kaya na sojin kasar ta Aljeriya, jim kadan bayan tashinsa da sanhin safiyar jiya Laraba.
A halin da ake ciki dai an shiga zaman makoki na kwanaki uku, a yayin da kuma za'a yi wa mamatan addu’a ta musamman a daukacin Masallatan kasar a gobe Juma’a.