Sama Da Bakin Haure 130 Ne Aka Ceto A Gabar Tekun Libiya
Kakakin Dakarun tsaron ruwan Libiya ya sanar da ceto sama da bakin haure 130 a arewa maso yammacin ruwan kasar.
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya nakalto Ayoub Qassem mai magana da yawun dakarun tsaron ruwan Libiya na cewa a jiya alhamis jami'n tsaron ruwan kasar sun samu nasarar ceto bakin haure masu kokarin shiga kasashen turai ta barauniyar hanya 137 a kusa da gabar ruwan garin Zawiya dake arewa maso yammacin kasar
Ayoub Qassem ya ce daga cikin wadanda aka ceton akwai mata da yara 19, kuma tuni aka basu taimakon gaggauwa tare da kula da lafiyarsu a sansanin dakarun ruwan na birnin Tripoli inda daga bisani aka meka su ga ma'aikatar dake kula da 'yan gudun hijra ta kasar.
Mafi yawan bakin haure na kasashen Afirka dake son zuwa kasashen Turai ta barauniyar hanya na amfani da kasar Libiya ne domin zuwa kasashen Turan.