Najeriya: An kashe Mutane 26 A Jahar Zamfara
Kamfanin dillancin labarun faransa ya bayyana cewa a jiya alhamis da dare ne mahara suka kashe masu hakar zinariya 26 a wani kauye na Jahar Zamfara
Wata majiya a yankin da lamarin ya faru ta ce; An kai harin ne akan wata kungiya da ake zaton suna aiki tare da sojojin gwamnati masu fada da kungiyoyin barayi da suke cikin dajin.
Tare da cewa da akwai sojoji da aka girke a cikin yankunan da ake yawaita kai hari a Jahar, tun a 2016 amma daga lokaci zuwa lokaci ana kai wa fararen hula hari tare da yi musu kisan gilla.
A cikin shekarun bayan nan dajukan da suke cikin jahar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya, barayin shanu masu dauke da manyan makamai suna tsananta kai wa kauyuka hare-hare.
Kasa da wata daya da ya gabata an kashe kusan mutane 100 tare da tilastawa wasu yin hijira.