An Tayar Da Bama-Bamai A Arewacin Kasar Mali.
Wata majiya ta kusa da MDD ta tabbatar da fashewar bama-bamai arewacin kasar Mali.
Kamfanin dillancin labaran Reutues ya nakalto shaidu na yankin da majiya ta kusa da MDD a wannan Lahadi na cewa an ji karar bashewar wasu ababe masu karar gaske da ake zaton bama-bamai ne a kusa da sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD da na Fasransa a garin Tombouctou dake arewacin kasar ta Mali.
To saidai har yanzu ba a bayyana hasarar rayuka ko dukiya da wannan tashin Bam ya janyo.
Kasar Mali ta fada cikin matsalar tsaro tun a 2012 bayan juyin mulkin da aka yi a kasar, da kuma kutsen masu tsaurin ra'ayi a arewacin kasar.
A shekarar 2013 kuma, Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD da na Faransa sun shiga kasar, to amma 'yan kasar na ganin cewa matakin da Dakarun ke dauka bai wadatar ba wajen tabbatar da tsaro a kasar.
A shekarar 2015, kungiyoyin masu dauke da makaman sun tsananta kai hare-harensu a tsakiya da kuma kudancin kasar ta Mali.