Fashewar Boma-Bomai A Arewacin Kasar Mali
Majiyar Majalisar dinkin duniya a kasar Mali ta bada labarin fashewar wasu abubuwa a arewacin kasar
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wata majiyar Majalisar dinkin duniya a biornin Timboktu daga arewacin kasar tana cewa an gi tashin wasu abubuwa masu karan gaske a sansanin sojojin Majalisar da ke cikin birnin.
Har yanzu dai rundunar Majalisar dingin duniya a cikin birnin MINUSMA bata yi wani karinn bayan a kan fashe-Fashen ba da kuma abinda ya haddasasu.
Amma majiyar sojojin kasar Faransa a birnin na Tumbuktu ta ce rokoki ne aka cilla kan sansanin sojojin MDD a cikin Birnin Amma babu wata barnan da suka yi na dukiya ko na rayuka. Wani dan kasuwa ma a birnin ya shaidawa rauters cewa ya ji karar fashewa a safiyar Lahadi, wacce ta fito daga anguwar da sojojin na Majalisar suke suka yi sansani.