Akidar Salafawa Ita Ta Bata Tunanin Al'umma A Kasashen Musulmi
(last modified Tue, 24 Apr 2018 06:48:34 GMT )
Apr 24, 2018 06:48 UTC
  • Akidar Salafawa Ita Ta Bata Tunanin Al'umma A Kasashen Musulmi

Shugaban Majalisar Koli ta musulinci a kasar Aljeriya ya bayyana cewa wanzuwar akidar salafiyanci ita ce ta bata tunanin al'umma a kasar da kasashen musulmi.

A yayin da yake jawabi a taron kasa da kasa mai taken taribyar musulinci a cibiyoyin gwamnati,a jiya Litinin  Abu Abdullahi Gulamullah shugaban majalisar koli ta musulinci a kasar Aljeriya ya ce kafin wanzuwar akidar salafiyanci, al'ummar musulmi a Duniya na rayuwa tare, ba tare da wata matsala ba, amma tun bayan da wannan mumunar akida ta fara wanzuwa a tsakanin al'ummar musulmi aka fara fuskantar rikici da zubar da jini a tsakanin al'ummar musulmi.

Shugaban Majalisar koli ta musulinci a Aljeriya ya ce addinin musulinci bai amince da tsatsauran ra'ayi ba, don haka ya bukaci al'ummar musulmi a Duniya da su kasance masu yada hakikanin koyarwar addinin musulinci na yafiya da kuma mutunta ra'ayin ko wani dan adam a duniya.

A cikin shekarun baya-bayan nan dai, kasar Aljeriyan ta fuskanci matsaloli da dama sanadiyar fatawa da wa'azi na maliman salafawa da wahabiyanci a kasar.

A jiya Litinin ne aka fara gudanar da  taron kasa da kasa mai taken taribyar musulinci a cibiyoyin gwamnati, da kuma ake sa ran za a kamala shi a wannan Talata a kasar Aljeriya.