Libiya : Marshal Haftar, Ya Koma Gida
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30324-libiya_marshal_haftar_ya_koma_gida
Jagoran sojojin gabashin Libya Marshal Khalifa Haftar ya koma gida jiya Alhamis, bayan shafe kusan makwanni biyu yana jinya a birnin Paris na Faransa.
(last modified 2018-08-22T11:31:45+00:00 )
Apr 27, 2018 04:31 UTC
  • Libiya : Marshal Haftar, Ya Koma Gida

Jagoran sojojin gabashin Libya Marshal Khalifa Haftar ya koma gida jiya Alhamis, bayan shafe kusan makwanni biyu yana jinya a birnin Paris na Faransa.

Wani wakilin kamfanin dilancin labaren Faransa na AFP, a Libiya, ya ce Khalifa Haftar ya sauka a filin jirgin sama na birnin Benghazi dake gabashin kasar, cikin murmushi, inda ya samu tarba daga mukarabansa.

An dai jima ana ta tababa kan halin da Marshal Khalifa Haftar, yake ciki, bayan rashin ganinsa a baina jama'a, inda har ma wasu jaridun Libiya dana duniya suka ambato mutuwarsa, duk da musu da kakakinsa da makusantasa da kuma wakilin musamman na MDD, a LIbiya, Ghassan Salame suka sha yi.

Kawo yanzu dai babu dalilai akan rashin lafiyarsa ko  iya adadin kwanakin da ya kwashe daidai yana jinya.

Tun dai bayan faduwar gwamnatin Kanal Muammar Ghadaafi a cikin 2011, Libiya ta kasa samun gindin zama, inda yanzu haka take fama da rikicin siyasa da kuma matsalar tsaro, kuma yanzu haka Libiyar na fama da gwamnatoci biyu, a daya bangare gwamnatin hadin kan kasa ta GNA dake samun goyan bayan kasashen duniya wacce ke a birnin Tripoli, sai kuma wacce ke a gabashi dake samun goyan bayan Marshal Khalifa Haftar.