Yarjejeniya A Bangaren Bunkasa Ilimi Da Bincike Tsakanin Iran Da Kenya
An rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ke nufin kara bunkasa harkokin ilimi da bincike tsakanin Iran da Kenya.
Bangaren hulda da jama’a na cibiyar bunkasa harkokin ilimi da a’adu ta kasar Iran ya sanar da cewa, karamin ofishin jakadancin Iran da ke kasar Kenya ne ya jagoranci tawagar Iran wajen rattaba hannu kan wannan yarjejeniya a kasar ta Kenya.
An rattaba hannu kan wannan yarjejeniya tsakanin kasashen Kenya da Iran ne domin gudanar da aikin hadin gwiwa ta fuskar bincike a kan harkokin addinai da tarihi.
Haka nan kuma za a rika shirya tarukan karawa juna sani a kan wasu muhimman lamurra da suka shafi bincike na ilimi a kan lamura da za su amfanar da kasashen biyu.
Kasar Kenya dai tana daya daga cikin kasashen nahiyar Afirka da suke da kyakkyawar alaka da Iran, ta fuskar siyasa, tattalin arziki da kasuwanci da kuma musayar ilimi.