May 03, 2018 05:35 UTC
  • 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da 'Yar Agaji A Somaliya_Red Cross

Kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red-Cross, ta sanar da cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wata jami'ar kiwan lafiya a wani gida dake Mogadisho babban birnin kasar Somaliya.

Jami'ar wacce 'yan asalin kasar Jamus ce an sace ta bayan wani hari da aka kai gidanta wajen karfe takwas agogon wurin a cikin daren jiya. 

Mukadanshin Darektan kungiyar ta Red-Cross a Somaliya, Daniel O'Malley, ya ce sun shiga damuwa sosai dangane da halin da abokiyar aikinsu ke ciki.

Ya kara da cewa jami'a ce mai hazaka, tana kuma aiki a ceton rayukan jama'a musamman raunana. 

Kungiyar ta Red-Cross ko CICR ta ce yanzu haka tana aiki da mahukuntan kasar don ganin an 'yanto matar. 

Tags