Jam'iyyar Al-Nahdha Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi Na Kasar Tunusia
Jam'iyyar Al-Nahda ta masu kishin addini a kasar Tunusiya ta lashe zaben kananan hukumomi da aka gudanar a kasar a jiya Lahadi lamarin da ke nuni da matsayin da take da shi a siyasar kasar.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo daya daga cikin kusoshin jam'iyyar ta Al-Nahda Lotfi Zitoun yana cewa sakamakon zaben da aka gudanar na nuni da cewa jam'iyyar ta su tana sama da jam'iyyar Nidaa da kaso 5 cikin dari na kuri'un da aka kada din.
Ana sa ran dai jam'iyyu biyu na al-Nahda da Nidaa din dai, wadanda su ne jam'iyyu biyu da suka hada kai wajen kafa gwamnatin hadaka ta kasar, za su ci gaba da mamaye fagen siyasa na kasar Tunusiyan tun bayan kifar da tsohuwar gwamnatin Ben Ali da aka kifar sakamakon boren 2011 da aka yi a kasar.
Jami'iyyun dai sun sha alwashin ci gaba da kiyaye hadin kan da ke tsakaninsu duk kuwa da 'yan sabanin da aka samu.