An Hana Firaministan Libiya sauka a birnin Tripoli
Kungiyoyin dake dauke da makamai a kasar Libiya sun rufe filin sauka da tashi na birnin Tripoli wanda hakan ya hana jirgin Firaministan hadin kai kasar sauka.
Tun bayan da aka samun labarin cewa Firaministan kasar ta Libiya Fa'iz Assiraj tare da tawagar ministocin Gwamnatinsa sun fito daga kasar Tunusiya za su kuma sauka a birnin Tripoli,kungiyoyin dake dauke da makamai suka rufe filin sauka da tashin na jiragen saman kasa da kasa dake birnin Tripoli wanda hakan ya Tilastawa Jirgin dake dauke da manbobin Gwamnatin komawa kasar Tunusiya.
A cewar Kungiyoyin masu dauke da makamai, sun rufe filin jiragen saman ne saboda harakokin tsaro. saidai a bangare guda Yusuf Kawaisa babban dararkatan filin jiragen saman na birnin Tripoli ya bayyana cewa a yau Litinin an dakatar da saukan jiragen ne na dan wani lokaci saboda harakokin tsaro, amma bayan wasu sa'o'i ,filin jirgin ya ci gaba da aiyukansa kamar yadda ya saba.
Kafin hakan dai, Ministan harakokin waje na Gwamnatin Libiyan da Duniya ba ta amince da ita, yayi baraznar hana Tawagar ministocin hakin kan kasar shiga birnin Tripoli, inda ya tabbatar da cewa ko da ya dace su yi amfani da makamai za su yi.
Ya zuwa yanzu dai Firaministan hadin kan kasar Libiya Fa'iz Assiraj tare da manbobin Gwamnatinsa na kasar Tunusiya.