Libya: An Fara Kai Farmaki Da Zummar 'Yanto Da Garin Darnah
Kwamandan runduwar Umar al-Mukhtar da ke karkashin sojojin Libya, Salim al-Rufai ya sanar da cewa; A yau litinin ne aka fara kai farmakin a karkashin umarnin Khalifa Haftar
Sojojin na Libya sun yi amfani da jiragen yaki wajen kai wa sansanonin 'yan ta'addan hari.
Jami'in hulda da jama'a na sojan Libya, Abdulkarim Sabrah, ya kira yi mutanen garin na Darnah da su bai wa sojojin hadin kai a yayin da su ke gudanar da ayyukansu.
Garin na Darnah ya dade a karkashin ikon kungiyar Majalisar Mujahidai ta Darnah, wacce reshe ne na kungiyar Al'ka'idah.
Tun a 2011 ne dai kasar Libya ta fada cikin rashin tsaro saboda tsoma bakin kasashen turai bisa jagorancin Amurka.
Khalifa Hafatar wanda shi ne babban hafsan sojan kasar ta Libya ne yake jagorantar fada da kungiyoyin da ke dauke da makamai a kasar.