Korar 'Yan Gudun Hijira Sudan Daga Nijar, Rashin Imani Ne_Amnesty
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30776-korar_'yan_gudun_hijira_sudan_daga_nijar_rashin_imani_ne_amnesty
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa (Amnesty International), ta yi tir da matakin hukumomin Nijar na korar 'yan Sudan dake neman mafaka a kasar.
(last modified 2018-08-22T11:31:49+00:00 )
May 13, 2018 14:34 UTC
  •  Korar 'Yan Gudun Hijira Sudan Daga Nijar, Rashin Imani Ne_Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa (Amnesty International), ta yi tir da matakin hukumomin Nijar na korar 'yan Sudan dake neman mafaka a kasar.

Kimanin 'yan Sudan 2,000 ne ke zaman neman mafaka a jihar Agadas dake arewacin Nijar, saidai a kwana nan hukumomin yankin sun kori 145 daga cikinsu zuwa iyakar kasar da Libiya, bisa a cewarsu dalilai na tsaro.

Kungiyar ta Amnesty ta danganta matakin hukumomin kasar ta Nijar da ''rashin imani'', taan bukatar hukumomin dasu kawo karshen irin wannan matakin.

Dama kafin hakan kungiyoyin agaji a yankin sun nemi hukumomin yankin dasu sassauta akan matakin.

Matakin da hukumomin yankin suka dauka dai ya biyo bayan karuwar masu gudun hijira mafi akasari 'yan Sudan dake gujewa rikicin kasar Libiya, wanda kuma ya sanya fargaba a zukatan mazauna birnin na Agadas inda suka bukaci hukumomin su dau mataki saboda tsaron lafiyar iyalansu.