Jami'an Tsaron Senegal Sun Hallaka Dalibin Jami'a
Taho mu gama tsakanin dali'an jami'a da jami'an tsaron kasar Senegal ya yi sanadiyar mutuwar dalibi guda tare kuma da jikkata mutane 20 na daban.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto ma'aikatar tsaron kasar Senegal na cewa a jiya Talata an yi taho mu gama tsakanin jami'an tsaro da daliban jami'a da suka taru a harabar jami'an Gaston Berger dake yankin St. Louis yayi sanadiyar mutuwar wani dalibin jami'ar mai shekaru 18 a duniya tare kuma jikkata wasu kimanin 20 na daban daga cikinsu akwai jami'an tsaro 18.
Baya ga wannan, sanarwar ta ce an kwashe kayayyakin dake cikin wasu gine ginan jami'ar.
Daliban jami'ar ta Senegal sun taru ne a harabar jami'ar St. Louis domin nuna rashin amincewarsu da rashin biyansu alawus- alawus na su, saidai hukumomin jami'an sun bukaci jami'an tsaron 'yan sanda da su tarwatsa su, lamarin da ya janyo hargizi har ta kai ga asarar rai.