Kwamitin Tsaro Ya Tsawaita Wa'adin Aikin Dakarun Sulhu Na AU A Somaliya
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya sake sabunta wa'adin aikin dakarun tabbatar da zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afirka a kasar Somaliya.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ba da labarin cewa a zaman da Kwamitin Tsaron yayi a daren jiya laraba, dukkanin membobin kwamitin sun amince da tsawaita wa'adin aikin dakarun tabbatar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka a kasar Somaliya har zuwa karshen watan Yuli mai kamawa.
A cikin kudurin da ya fitar a jiyan kwamitin tsaron ya janye bukatar da ya gabatar tun da fari kan rage dakarun tabbatar da zaman lafiyan, kamar yadda kuma ya bukaci babban sakataren MDD da ya ci gaba da ba da goyon baya ga dakarun na Afirka.
Kungiyar Tarayyar Afirkan dai ta tura dakarun nata kasar Somaliya ne da nufin tabbatar da zaman lafiya da kuma fada da 'yan kungiyar Al-Shabab da suke rike da wasu bangarori masu yawa na kasar a wancan lokacin sakamakon gazawar sojojin kasar.