'Yan Ta'adda Na Garkuwa Da Mutane A Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30952-'yan_ta'adda_na_garkuwa_da_mutane_a_libiya
Hukumomin kasar Libiya sun yi gargadi kan yadda 'yan ta'adda ke amfani da fararen hula domin kare kansu a gabashin kasar
(last modified 2018-08-22T11:31:51+00:00 )
May 20, 2018 07:54 UTC
  • 'Yan Ta'adda Na Garkuwa Da Mutane A Libiya

Hukumomin kasar Libiya sun yi gargadi kan yadda 'yan ta'adda ke amfani da fararen hula domin kare kansu a gabashin kasar

Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya nakalto Ahmad Musa Rizkull...daya daga cikin sojojin kasar Libiya na cewa 'yan ta'adda a birnin Derna dake gabashin kasar na kokarin yin amfani da fararen hula domin kare kansu daga farmakin sojojin kasar.

A cikin 'yan kwanakin nan Janar Khalifa Haftar babban hafsan sojojin kasar Libiya ya bada umarnin tsarkake garin Derna daga mamayar kungiyoyin 'yan ta'adda.

Rahotani dake fitowa daga filin daga sun habarta cewa 'yan ta'aaddar na sanya kananen yara sahun farko yayin fafatawa da Sojojin kasar ta Libiya a Derna.

Tun a watan Favrayun 2011 ne a daidai lokacin da aka kifar da gwamnatin marigayi kanal Mu'amar Kaddafi, 'yan ta'addar Mujahidun dake a matsayin wani bangare na kungiyar AlQa'ida suka mamaye garin Derna dake gabashin kasar ta Libiya.

A halin da ake ciki dai garin Derna shi ne gari na karshe dake hanun 'yan ta'adda tun bayan da Khalifa Haftar ya fara jagorantar yaki da 'yan ta'adda a shekarar 2014.