Harin Ta'addanci Ya Hallaka Mutum 2 A Arewa Maso Yammacin Aljeriya
An Kai harin ta'addanci a jahar Sidi Bel Abbès dake arewa maso yammacin kasar Aljeriya, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutun biyu.
Cikin rahoton da ta buga a wannan talala, jaridar Alsharq ta habarta cewa Ladanai biyu ne na wani masallacin jahar Sidi Bel Abbès suka rasa rayukansu sanadiyar wani harin ta'addanci da aka kai masallacin.
Ya zuwa yanzu babu wani gungu ko kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, kuma an kasa gano manufar da ta sanya aka kai wannan ta'addanci.
kafin hakan dai, a ranan 31 ga watan Augustan 2017, an kai wani harin ta'addanci a garin Tiaret, lamarin da ya yi sanadiyar hallakar jami'an 'yan sanda biyu da dan ta'adda guda.
A halin da ake ciki kasar Aljeriya na fama da matsalar rashin tsaro da rikicin siyasa, da kuma fuskantar hare-haren ta'addanci a kasar.