Kamaru: An Kashe Mutum 34 A Yankin 'Yan Aware
Rahotanni daga kasar Kamaru na cewar akalla yan aware 34 aka kashe a garin Menka dake Yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi
Kamfanin dillancin labaran kasar faransa ya nakalto Agbor Balla Nkongho, wani lauya mai kare hakkin Bil Adama a Yankin na cewa an samu gawawaki 34 yammacin juma’a, ba tare da sanin wanda ya kashesu ba,kuma Wannan shine tashin hankali mafi muni da aka samu a yankin tun bayan barkewar tashe-tashen hankulan da ke da nasaba da neman yanci.
A nasa bangare Kakakin sojin kasar Kanar Didier Badjeck ya shaida wa manema labarai cewar jami’an tsaro sun yi arangama da wasu mutane da suka taru a wani otel a Menka da ake zargin yan aware ne.
Tun a farko a wannan shekara ta 2018 kici ya billa a yankin masu magana da turancin inglishi, lamarin da ya yi sanadiyar hallakar sojojin kasar 28.