An Cimma Yarjejeniyar Tsaro Tsakanin Kasashen Libiya, Nijar, Sudan Da Chadi
(last modified Sat, 02 Jun 2018 18:23:27 GMT )
Jun 02, 2018 18:23 UTC
  • An Cimma Yarjejeniyar Tsaro Tsakanin Kasashen Libiya, Nijar, Sudan Da Chadi

Gwamnatin kasar Libiya ta sanar da sanya hannu kan yarjejjeniyar tsaro na kare iyakokin kasar da kasashen Nijar, Sudan da Chadi.

Jaridar Alyaumu-sabi'i ta nakalto ministan harakokin wajen Lbiya Mohammad Tahir Sialah a wannan assabar na cewa kasarsa ta cimma yarjejjeniyar aiki tare da kuma karfafa tsaro da sanya ido a kan iyakar kasar da kasashen Nijer, Sudan da kuma Tchadi.

Bayan cimma wannan yarjejjeniya, ministan harakokin wajen Libiya ya ce kasarsa za ta yi iya nata kokari, ta hanyar korewa da kuma tajrubar da take da shi tare da hadin kan al'ummar kasar wajen kare wannan yarjejjeniya, domin tabbatar da sulhu, da tsaro da kuma kyautata alakar makwabtaka, da bunkasa tattalin arziki da zamantakewa tsakanin kasashen.

Akwai dai kungiyoyin fasa kwabri da suka hada da masu safarar mutane, da masu fasa kwabrin man fetir a tsakanin iyakokin  wadannan kasashe hudu.