Sojojin Libya Suna Daba Da Kwace Garin Darni Daga Hannun Yan Ta'adda
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31530-sojojin_libya_suna_daba_da_kwace_garin_darni_daga_hannun_yan_ta'adda
Wata majiyar sojojin kasar Libya ta bayyana cewa sojojin kasar karkashin Janar Halifa Haftar mai ritaya suna daba da kwace garin Darne daga gabacin kasar daga hannun yan ta'adda.
(last modified 2018-08-22T11:31:56+00:00 )
Jun 08, 2018 06:42 UTC
  • Sojojin Libya Suna Daba Da Kwace Garin Darni Daga Hannun Yan Ta'adda

Wata majiyar sojojin kasar Libya ta bayyana cewa sojojin kasar karkashin Janar Halifa Haftar mai ritaya suna daba da kwace garin Darne daga gabacin kasar daga hannun yan ta'adda.

Tashar talabijin ta "Skynews Arabi" ta nakalto majiyar sojojin kasar Libya karakshin janar Halifa haftar tana cewa a halin yanzu sojojin sun yiwa yan tawaye a garin Darne kawanya ta ko ina, kuma ana saran nan ba da dadewa ba za'a kwace garin daga hannunsu. 

Tun tsakiyar watan mayun da ya gabata ne sojojin kasar ta Libya suka fara fafatawa da mayakan "Shuran Mujahidan Darne" wadanda suke iko da garin Darne tun shekara ta 2011, kuma ya zuwa yanzu an kashe fararen hula 17 inda biyu daga cikinsu yara kanana ne.

Tun cikin watan Febrerun shekara ta 2011 ne "Majalisar Shuran Mujahidan Darne" wacce take da dangantaka da kungiyar Alqaeda ta kwace iko da garin Darne, kuma tun lokacin ne suke cin karensu ba babbaka a kan mutanen garin.