Libya : Shugaban Gwamnatin Hadaka Ya Samu Isa Tripoli
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3163-libya_shugaban_gwamnatin_hadaka_ya_samu_isa_tripoli
Shugaban gwamnatin hadaka na kasar Libya dake samun goyan bayan MDD Fayez al-Sarraj ya isa birnin Tripoli a wannan Laraba ba tare da fuskantar wata turjiya ba.
(last modified 2018-08-22T06:58:03+00:00 )
Mar 30, 2016 11:52 UTC
  • Libya : Shugaban Gwamnatin Hadaka Ya Samu Isa Tripoli

Shugaban gwamnatin hadaka na kasar Libya dake samun goyan bayan MDD Fayez al-Sarraj ya isa birnin Tripoli a wannan Laraba ba tare da fuskantar wata turjiya ba.

Mr Sarraj dake samun rakiyar wasu membobin kwamitin shugabancin kasar ya isa a sansanin jiragen ruwan soji na Tripoli inda har ma ya gana da hafsoshin sojin sansanin.

Shugaban gwamnatin wanda ya kasance har jiya a birnin Tunis ya isa Tripoli ne a cikin jirgin ruwa soji kasar ta Libya a cikin kwararen matakan tsaro, kuma a isar sa ya samnu tarbe daga mahukuntan yankin ciki har da ministan cikin gidan na gwamnatin da duniya bata amunce da ita ba.

Hukumomin Tripoli da duniya bata amunce da su ba sunyi dai ta kokarin hana shugaban gwamnatin hadakar isa birnin ta ko wanne hali.

An dai kafa gwamnatin hadakar ne a shiga tsakanin MDD a wata jarjejeniya da aka rattaba ma hannu a watan Disamba bara a kasar Marocco, da zumar kawo karshen rikicin dake tsakanin gwamnatocin Tripoli da Tobruk da ko wanne ke ikirarin shugabancin wannan kasa data shiga rudani tun bayan kifar da gwamnatin mirigayi kanal Ghadafi.