Libya: An Kai Hare-haren Kunar Bakin Wake A Garin Darnah
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31666-libya_an_kai_hare_haren_kunar_bakin_wake_a_garin_darnah
Jami'in hulda da jama'a na sojan kasar Libya, Halifah al-Ubaidy ya ce; Da safiyar yau talata ne aka kai hare-haren kunar bakin waken biyu a yankin Shaiha da ke garin Darnah.
(last modified 2018-08-22T11:31:58+00:00 )
Jun 12, 2018 19:08 UTC
  • Libya: An Kai Hare-haren Kunar Bakin Wake A Garin Darnah

Jami'in hulda da jama'a na sojan kasar Libya, Halifah al-Ubaidy ya ce; Da safiyar yau talata ne aka kai hare-haren kunar bakin waken biyu a yankin Shaiha da ke garin Darnah.

Al-Ubaidy ya kuma kara da cewa; Kawo ya zuwa yanzu da akwai fararen hula da dama da su ka kwanta dama, yayin da wasu kuma su ka jikkata.

Harin kunar bakin waken na yau ya faru ne a daidai lokacin da sojojin Libya a karkashin Halifa Haftar suke samun galaba akan 'yan ta'addar garin na Darnah.

Tun a watan Febrairu na 2011 ne dai kungiyar da ake kira; Majalisar Mujahidan Darnah' ta shimfida iko a garin na Darnah. Ita dai kungiyar wani reshe ne na kungiyar 'yan ta'adda ta al-ka'ida.

A farkon watan Mayu ne dai sojojin da ke biyayya ga Halifah Haftar su ka fara kai wa garin hari da zummar kwace ido da shi.