Kamaru : An Cafke 'Yan adawa sama da 60 A Yaounde
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3169-kamaru_an_cafke_'yan_adawa_sama_da_60_a_yaounde
'Yan sanda a Kamru sun cafke 'yan adawa kimanin 60 saboda kiran wani gangami a Yaoude babban birnin kasar domin nuna kin amuncewar su da yunkurin gyarran fuska da mahukuntan kasar ke son yiwa kundin tsarin mulki domin gusa lokacin zaben shugaban kasa.
(last modified 2018-08-22T06:58:03+00:00 )
Mar 30, 2016 12:46 UTC
  • yan sanda kamaru
    yan sanda kamaru

'Yan sanda a Kamru sun cafke 'yan adawa kimanin 60 saboda kiran wani gangami a Yaoude babban birnin kasar domin nuna kin amuncewar su da yunkurin gyarran fuska da mahukuntan kasar ke son yiwa kundin tsarin mulki domin gusa lokacin zaben shugaban kasa.

Mafi yawa daga cikin 'yan adawan an cafke su ne jiya Talata a lokacin da suka kokarin halartar wani taron manema labarai da jam'iyun adawa na kasar suka kira kamar yadda Christophe Bobiokono mamba a kwamitin kare hakin bil adama na kasar ya tabbatarwa da kanfanin dilancin labaren AFP.

A shekara 2018 aka shirya gudanar da babban zaben wannan kasa sai dai a cewar 'yan adawa gwamantin na yunkurin gusa lokacin zaben a boye.

'yan adawa dai sun ce majalisar dokokin kasar na son yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima saboda mutun guda wato shugaba Paul Biya daya shafe shekaru 34 kan karagar mulki wannan kasa.

Wasu rahotanni daga kasar sun ce an fara sakin wasu daga cikin 'yan adawan, wanda daga bisani suka samu yiwa 'yan jarida magana akan titi koda yake anan ma 'yan sanda sun tarwatsa su da hayaki mai sa kwalla.