'Yan Tawaye Sun Kai Hari Kan Cibiyoyin Man Fetir A Gabashin Libiya
Majiyar tsaron Libiya ta sanar da mutuwar mutun 34 yayin fafatawa tsakakin 'yan tawaye da dakarun Khalifa haftar a gabashin kasar.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, majiyar tsaron Libiya ta sanar da cewa cikin sa'o'i 48 da suka gabata, an kashe sojoji 14 da kuma 'yan tawaye 20 yayin da ake fafatawa tsakanin Sojojin kasar karkashin jagorancin Khalifa Haftar da 'yan tawayen da suka kai farmaki kan cibiyoyin man fetir din kasar a gabashin kasar.
'Yan tawayen sun kai hari ne a cibiyoyin man dake karkashin kulawar dakarun Khalifa Haftar dake gabashin kasar daga cikinsu, har da na tashar ruwan Ra'asu Lanuf da Sadra, inda suka sanya wuta kan wata ma'aji'ar man fetir din dake yankin.
A cewar majiyar tsaron ta Libiya 'yan tawayen birnin Bangazi ne da a shekarar da ta gabata, dakarun khalifa Haftar suka fatattake su daga birnin, sune suka kai harin.
A nata bangare kamfanin Man fetir na NOC ya kwashe dukkanin ma'aikatansa daga yankin Hilalu-Nafty dake gabashin kasar sannan kuma ya ayyana dokar tabace a cibiyoyin hako da man fetir na gabashin kasar.
A cewar ma'aikatar man fetir din kasar, harin na 'yan tawaye ya janyowa kasar hasarar ganga dubu 240, daga cikin man fetir din da kasar take fitowa ko wata rana.