Libya: An Tseratar Da 'Yan Gudun Hijira 191 Daga Nutsewa A Ruwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31850-libya_an_tseratar_da_'yan_gudun_hijira_191_daga_nutsewa_a_ruwa
Jami'an tsaro masu kula da iyakokin ruwan kasar Libya ne su ka sanar da ceto da 'yan ci-rani daga halaka.Tashar talabijin din France 24 ta ba da labarin cewa; An ceto mutanan ne a yankuna alzawiyah da kuma yammacin birnin Tripoli
(last modified 2018-08-22T11:31:59+00:00 )
Jun 19, 2018 12:58 UTC
  • Libya: An Tseratar Da 'Yan Gudun Hijira 191 Daga Nutsewa A Ruwa

Jami'an tsaro masu kula da iyakokin ruwan kasar Libya ne su ka sanar da ceto da 'yan ci-rani daga halaka.Tashar talabijin din France 24 ta ba da labarin cewa; An ceto mutanan ne a yankuna alzawiyah da kuma yammacin birnin Tripoli

Sai dai sanarwar ta ce an sami mutane biyar a tsakanin 'yan gudun hijirar da su ka rasa rayukansu a gabar ruwan da ke yammacin birnin Tripoli.

Sanarwar ta ci gaba da cewa mutanen da aka ceto sun fito ne daga kasashe daban-daban na Afirka da kuma kasashen larabawa.

Masu fataucin mutane suna amfani da rashin tsaron da kasar Libya take fama da shi domin samun riba daga jigilar 'yan ci-rani. A kowace shekara ta Allah dubban mutane ne suke rasa rayukansu sanadiyyar hatsurran da suke fuskanta na nutsewa a ruwa.