An Cabke 'Yan Ta'addar ISIS Uku A Gabashin Libiya
Kakakin ma'aikatar tsaron garin Shahhat na gabashin Libiya ya sanar da cabke 'yan ta'addar ISIS uku.
Kamfanin dillancin labaran Pars ya nakalto Hassan Abu Karim kakakin ma'aikatar tsaron garin Shahhat na kasar Libiya na cewa dakarun tsaron kasar sun samu nasarar cabke wasu 'yan ta'adda guda uku masu alakar da kungiyar ISIS, bayan ficewarsu daga garin Derna na gabashin kasar.
Hassan Abu Karim ya ce wadannan 'yan ta'adda uku da aka cabke sun amsa laifinsu da kisa, satar mutane, watsa mumuntar akidar ta'addanci a tsakanin mazauna yankin da kuma fafatawa da jami'an tsaron kasar a anguwanin Haliya da Fata'ih na garin Derna dake gabashin kasar.
Tun a shekarar 2011 ne kasar Libiya ta fada cikin rikici, bayan Amurka da kungiyar tsaron Nato suka taimakawa 'yan tawaye wajen kifar da gwamnatin marigayyi kanal Mu'ammar kaddafi,wanda hakan ya sanya 'yan ta'adda daga kasashe Duniya da dama suka yi wa kasar kawanya, sannan suka kafa tungarsu a wasu yankunan kasar.