Kamaru: Mutane 4 Sun Kwanta Dama A Yakin Masu Magana Da Ingilishi
Wasu masu dauke da makamai ne su ka kai hari akan 'yan sanda masu sintiri a yankin na masu magana da harshen turanci ingilishi wanda ya kashe mutane 4
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato majiyar tsaron kasar Kamaru na cewa;An kai harin ne a garin Bamenda da ke gundumar Mezam. Daya daga cikin wadanda su ka rasa raukansu ne dan sanda, saura kuma fararen hula. Har ila yau rahoton ya ce wasu karin 'yan sandan 4 sun jikkata.
Tuni dai jami'an tsaron kasar su ka tsananta yin sintiri a yankin domin gano maharan.
Yankunan da suke magana da harshen turancin Ingilishi a arewa maso yammacin kasar da kuma kudu maso yamma akan iyaka da Najeriya, sun yin kira na ballewa domin kafa kasa mai cin gashin kanta.
Masu magana da harshen na Ingilshi a kasar Kamaru suna a matsayin kaso 20% na jumillar al'ummar kasar mai mutane miliyan 20.