Libya: Haftar Ya Bada Sanarwar Kwace Garin Durnah Daga Hannun Yan Ta'adda
Janar Halifa Haftar mai ritaya, wanda kuma yake iko da gabacin kasar Libya ya bada sanarwan cewa dakarunsa sun kwace garin darne daga hannun yan ta'adda a yankin.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto Janar Halifa Haftar mai ritaya yana fadar haka a jiya a wani jawabin da yayiwa mutanen yankin a wata tashar Talabijin. Haftar ya yi alkawarin tabbatar da cewa zama lafiya mai dorewa ta dawo dawo a garin na Darne.
Kafin haka dai kungiyar yan ta'adda ta "Mujahudun Darne " ne suke iko da garin tun bayan faduwar gwamnatin kazzafi a shekara ta 2011. Kungiyar ta "Mujahidan Darne" tana da dangantaka da kungiyar yan ta'adda ta Daesh
Khalifa haftar dai bai amince da gwamnatin fa'iz Suraj a birnin Tripoli ba, mai makon haka yana goyon bayan gwamnati da majalisar dokoki da Tabruq.
A ranar 7 ga watan Mayun da ta gabata ce sojojin Janar Haftar suka fara fafatawa da yan tawayen da nufin kwato garin daga hannunsu.