An Kai Wa Sojojin Faransa Hari A Mali
Rahotannin dake cin karo da juna Mali, na cewa an kai wa sojojin Faransa hari a yankin Gao a tsakiyar kasar daga arewaci.
Babu dai karin bayyani na alkalumma hasara rayuka ko raunana da aka samu kawo.
Bayanai sun ce wasu 'yan bindiga ne cikin mota suka yi wa sojojin na rundinar Barkhane kofar raggo, kan hanyarsu ta zuwa lardin Burem, kamar yadda wata majiyar tsaron sojin kasashen yamma ta tabbatar wa da kamfanin dilancin labaren AFP.
Wannan harin dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan harin kunan bakin waken da ya yi ajalin mutum uku, da suka hada da sojoji biyu a shalkwatar rundinar G5 Sahel dake tsakiyar kasar ta Mali wacce aka kaddamar a bara don yaki da ta'addanci.
A gobe Litini ce aka tsara shugaba Emanuel macron na Faransa zai gana da shugabannin kasashen gungun na G5 Sahel, (Mauritania, Mali, Burkina Faso, Nijar da kuma Chadi), inda zasu tattaunawa kan mi ke hana ruwa gudu wajen aiwatar da aikin rundinar ta G5 Sahel.