Libiya : Kwale-kwale Ya Bata Da Mutane 63
Jul 03, 2018 05:39 UTC
Rundinar sojin ruwan Libiya, ta ce kimanin bakin haure 63 ne aka kyautata zaton sun bata, bayan nutsewar kwale-kwalen da suke ciki a tekun Bahar Rum.
Wannan dai ya sanya adadin mutanen da suka bata zuwa 170 tun daga ranar Juma'a data gabata.
Mutanen 63, sun bata ne, bayan nutsewar kwale kwalen da suke ciki a ranar Lahadi data gabata, a gabar ruwan ruwan Libiya, kamar yadda kakakin rundinar sojin ruwan Libiya ya tabbatar wa da kamfanin dilancin labaren AFP.
Janar Ayub Kacem, ya ce, sun samu labarin ne daga wasu bakin haure 41 wadanda aka ceto, saboda suna sanye da rigar ceto mai hana nutsewa a ruwa.
Jami'an gabar ruwan sun ce basu samu gawawarkin mutane ba a wajen da lamarin ya auku ba.
Tags