EU Zata Kakabawa Wasu Mayan Jami'an Libya Takunkumi
-
Frederica Mogereni babbar jami\\\\\\\'ar diflomatsiya ta kungiyar EU
kungiyar tarayya Turai na nazarin kakabawa wasu mayan jami'an Libya uku takunkumi saboda anniyar su ta neman toshe gwamnatin hadaka dake samun goyan bayan MDD.
Wadanan takunkuman sun shafi shugaban majalisar dokokin Tobruk Aguila Saleh, da shugaban majalisar Tripoli Nouri Abou Sahmein da kuma shugaban gwamnatin Tripoli Khalifa al-Ghweil.
A wannan juma'ar ce ake sa ran wadanan takunkuman zasu fara aiki kan wadanan jami'an kamar yadda wasu majiyoyin kungiyar ta EU suka tabbatarwa da kanfanin dilancin labaren AFP.
A shekaren jiya Laraba ne shugaban gwamnatin hadaka dake samun goyan bayan MDD Fayez al-Sarraj ya samu isa birnin na Tripoli, saidai jin kadan bayan isar tasa hukumomin birnin da duniya bata amunce dasu ba suka umurce shi daya fice daga birnin, lamarin da ake ganin zai iya kawo cikas ga yunkurin samar da zamen lafiya a wannan kasa, da yanzu haka ke da gwamnatoci guda uku.
Rahotanni daga kasar ta Libya sun ce harkokin kasuwanci sun tsaya cik, yayin da al'umma wannan kasa ke cikin zaman dar-dar.