Sojojin Aljeriya Sun Fara Kai Gagarumin Hari Akan Iyaka Da Kasar Tunisiya
Bayan harin ta'addancin da aka kai a yankin Jandubah, sojojin Aljeriya sun fara kai gagarumin hari aka iyaka da Tunisiya domin farautar 'yan ta'adda
Kamfanin dillancin labarun "Iran' ya nakalto cewa;Farmakin da sojoijin na Aljeriya suke kai wa ya shafi gundumomin Tabsha, Suq Ahras, da al-wadi.Rahoton ya ci gaba da cewa da akwai sojoji da adadinsu ya kai 2000 a cikin farmakin.
A gefe daya majiyar tsaro daga kasar Tunisiya ta ce 'yan ta'adda sun kai wani harin a gundumar Jandubah da ke arewa maso yammacin kasar a iyaka da kasar Aljeriya.
A cikin wannan makon an kai wani hari a kan iyaka wanda ya ci rayukan sojoji shida.
Tun daga 2011 ne dai kasar Tunisiya mai makwabtaka da kasar Aljeriya take fama da matsalar 'yan ta'adda da ta'addanci. Da akwai fiye da mutane dubu biyar 'yan asalin kasar ta Tunisiya da suka yi yaki da kungiyoyin Da'esh da al-ka'ida.