Shugaban Kwamitin AU Na Ziyara A Kamaru
(last modified Thu, 12 Jul 2018 14:32:44 GMT )
Jul 12, 2018 14:32 UTC
  • Shugaban Kwamitin AU Na Ziyara A Kamaru

Shugaban kwamitin kungiyar tarayya Afrika ta (AU), Musa Faki Mahamat, ya fara wata ziyara yau Alhamis, a Jamhuriya Kamaru, inda kuma zai gana da shugaban kasar, Paul Biya, kamar yadda fadar shugaban kasar Kamarun ta sanar.

Wannan dai ita ce ziyarar Mista Faki, a wannan kasa ta Kamaru, tun bayan zabensa a matsayin shugabancin kwamitin kungiyar ta AU, a watan Janairu na shekara 2017.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta Kamaru ta fitar, bata yi karin haske ba, kan ziyarar jami'in, amma masu sanya ido na ganin cewa ziyarar na da girman gaske ta fuskar siyasa, idan akayi la'akari da rikicin da kasar Kamaru ke fama dashi, musamman a yankin arewa maso yamma da kuma kudu maso yamma, yankuna biyu na masu magana da turancin Ingilishi dake fafatukar ballewa.

A ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa na wannan shekarar ce, al'umma kasar ta Kamaru ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa, wanda kuma rikicin da yankunan ke fama dasu ke zaman babban kalubale ga zaben.