An Jaddada Wajabcin Warware Matsalar Kasar Libya Ta Ruwan Sanyi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32346-an_jaddada_wajabcin_warware_matsalar_kasar_libya_ta_ruwan_sanyi
Manzon Majalisar Dinkin Duniya aa musamman akan Kasar Libya Ghassan Salamah neya bayyana hakan, yana mai cewa tsoma bakin kasashen waje ya sake haddasa sabani
(last modified 2018-08-22T11:32:06+00:00 )
Jul 16, 2018 06:54 UTC
  • An Jaddada Wajabcin Warware Matsalar Kasar Libya Ta Ruwan Sanyi

Manzon Majalisar Dinkin Duniya aa musamman akan Kasar Libya Ghassan Salamah neya bayyana hakan, yana mai cewa tsoma bakin kasashen waje ya sake haddasa sabani

Ghassan Salamah ya kara da cewa sake warware rikicin na kasar Libya yana da bukatuwa da lokaci mai tsawo saboda yadda aka karkatsa kasar.

Har ila yau manzon na Majalisar Dinkin Duniya ya ce; Da akwai bukatar a sake fasalta sojojin kasar haka nan kudaden shiga na man fetur da kuma tsarin karatun kasar.

Libya ta tsunduma cikin rashin tsaro ne a 2011 da kasashen turai su ka kifar da gwamnatin Mua'ammar khaddafi.

Da akwai kungiyoyi masu yawa da suke dauke da makamai a cikin kasar ta Libya da su ka hada da Da'esh da al'ka'ida.