Nijar Za Ta Aike Da Sojoji 842 A Cikin Tawagar (MINUSMA)
(last modified Tue, 17 Jul 2018 05:50:52 GMT )
Jul 17, 2018 05:50 UTC
  • Nijar Za Ta Aike Da Sojoji  842 A Cikin Tawagar (MINUSMA)

Jamhuriya Nijar ta ce za ta aike da wata bataliyar sojojinta data kunshi dakaru 842 a cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya cewa da (MINUSMA) a kasar Mali.

Za'a dai jibge sojojin ne a arewacin Mali, domin tabbatar da ayyukan tsaro da zaman lafiya kamar yadda ka'idojin MDD suka tanada.

Wannan dai shi ne karo na shida da Nijar ta aike wa da bataliyar soji a cikin tawagar ta (MINUSMA), domin yaki da ta'addanci a makobciyar kasar Mali, kuma a cikin wannan aikin ta rasa sojojinta da dama.

Kamfanin dilancin labaren Xinhua, wanda ya rawaito labarin ya ambato babban habsan habsohsin sojin kasar ta Nijar na cewa, sojojin sun samu horo da kuma duk kayan aikin da suke bukata domin tafiyar da aikinsu. 

Kasashen Nijar da Mali dai na fuskantar matsalar tsaro data hada da mayakan dake ikirari da sunan jihadi.