Ministar Tsaron Faransa Na Ziyara Nijar Don Karfafa Wa Kungiyar G5 Sahel
Jul 20, 2018 10:43 UTC
Ministar tsaron kasar Faransa, Florence Parly, ta fara wata ziyarar aiki a Jamhuriya Nijar, domin karfafa wa kungiyar yaki da ta'addanci ta G5 Sahel.
Wannan dai shi ne karo na bakwai da ministar tsaron faransar ke ziyartar wannan yankin.
Ministar ta samu ganawa da shugaban kasar ta Nijar, Alhaji Isufu Mahamadu, wanda shi ne shugaban kungiyar ta G5 Sahel, da kuma takwaranta na Nijar Kalla Muntari.
Manufar ziyarar dai ita ce karfafa wa, kungiyar ta G5 Sahel akan yadda rundinar hadin gwiwa ta kasashen da suka da (Mali, Burkina Faso, Nijar Chadi da kuma Mauritania) zata fara aiki gadan gadan.
Tags