An Fitar Da Jerin Sunayen 'Yan Takara A Zaben Kamaru
(last modified Sat, 21 Jul 2018 05:46:49 GMT )
Jul 21, 2018 05:46 UTC
  • An Fitar Da Jerin Sunayen 'Yan Takara A Zaben Kamaru

A Kamaru, an fitar da jerin sunayen 'yan takara 28 dake neman fafata wa a zaben shugaban kasar na ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa.

Daga cikin 'yan takarar akwai shugaban kasar mai ci Paul Biya, da kuwa wadanda ya taba fafata wa dasu a baya, sai kuma wasu sabbin fuskoki. 

Akwai sasanun 'yan takara da suka tsaya a zaben wadanda suka hada da Adamu Ndam Njoya, dan shekaru 76 na Jam'iyyar (UDC) da Garga Haman Adji na jam'iyyar (ADD) daga cikin sanannun 'yan takara a kasar.

Yawan 'yan takarar dai ya ragu sosai idan aka kwatantan da zaben kasar na 2011, inda 'yan takara 40 suka ajiye takararsu.

Nan gaba ne hukumar zaben kasar za ta bayyana sunayen 'yan takarar da aka amince dasu, wadanda kuma akayi watsi da takararsu suna da damar shigar da kara gaban majalisar tsarin mulkin kasar.