'Yan Boko Haram Sun Kai Hari A Yankin Tabkin Tchadi
Kimanin mutum 18 ne suka rasa rayukansu a wani hari da mayakan boko haram suka kai yankin tabkin Tchadi.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto jami'an tsaron yankin tabkin tchadi na cewa ko baya ga mutanan da suka rasa rayukansu akwai wasu biyu da suka jikkata, sannan kuma sun yi awan gaba da wasu mata kimanin 10.
A cikin 'yan kawanakin nan dai mayakan boko haram din sun tsananta kai hare-hare a kasashen dake yankin tabkin tchadi, inda Ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Niger a cikin daren jiya Asabar ta sanar da cewa: Mayakan kungiyar Boko Haram sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan sansanin sojin Niger da ke yankin jihar Diffa a shiyar kudu maso gabashin kasar, inda sojoji suka maida martani kan gungun 'yan ta'addan tare da kashe akalla 10 daga cikinsu.
Ko baya ga hakan, rahotani dake fitowa daga Najeriya na cewa mayakan boko Haram sun yi wa sojojin kasar kwantar bauna ne a Babban Gida jiya Asabar, garin da ba ya da nisa da sansanin sojojin da aka taba kai wa hari a jihar Yobe.
Akalla sojoji 28 aka ruwaito an kashe a harin da aka kai a sansanin inda kuma mayakan na Boko Haram suka kwashi makamai. Amma rundunar sojin ta musanta cewa an kashe jami'anta a harin.