Faransa Na Karin Matsin Lamba Ga Libiya Kan Zabe
A yayin ganawarsa da manyan 'yan siyasar Libiya, Ministan harakikin wajen Faransa ya ce dole ne kasar ta tsara gudanar da zabe a watan Dicembar 2018.
Kamfanin dillancin Labaran France Press ta nakalto Jean-Yves Le drian ministan harakokin wajen kasar Faransa a yayin tattaunawar da ya yi da Firaministan kasar Libiya Fa'iz Siraj jiya Litinin a birnin Tripoli babban kasar Libiya na cewa bangarorin 'yan siyasar Kasar ta Libiya sun yi alkawarin gudanar da zaben Shugaban kasar da na 'yan Majalisa kafin karshen wannan shekara ta 2018.
Le Drien ya kara da cewa gudanar da zabe shi ne bukatar 'yan kasar Libiya a wannan yanayi da ake ciki.
Baya ga Piraministan kasar ta Libiya Fa'iz Siraj, Khalid Mashri, shugaban Majalisar Dokokin kasar dake zama a Tripoli, da Janar Khalifa Haftar, Babban Hafsan sojojin kasar, da Akilah Salih Shugaban Majalisar dokokin kasar dake zama a birnin Tabruk dukkaninsu sun yi alkawarin gudanar da zaben shugaban kasar kafin ranar 10 watan Disemba a yayin ganawar da suka yi da ministan harakokin wajen na Faransa Jean-Yves Le drian, sannan sun yi masa alkawarin cewa cibiyoyin gwamnatin kasar ne musaman ma babban bankin kasar za a mekawa ragamar kula da kudaden da kasar take samu ta hanyar man fetir.