An Kai Hari Kan Ofishin 'Yan Sanda A Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32463-an_kai_hari_kan_ofishin_'yan_sanda_a_libiya
Majiyar tsaron Libiya ta sanar da cewa wasu gungun 'yan ta'adda sun kai hari kan ofishin 'yan sanda na garin Ajdabiya dake gabashin kasar
(last modified 2018-08-22T11:32:09+00:00 )
Jul 24, 2018 19:17 UTC
  • An Kai Hari Kan Ofishin 'Yan Sanda A Libiya

Majiyar tsaron Libiya ta sanar da cewa wasu gungun 'yan ta'adda sun kai hari kan ofishin 'yan sanda na garin Ajdabiya dake gabashin kasar

Kamfanin dillancin labaran Fars ya nakalto majiyar tsaron Libiya na cewa a safiyar yau Talata, wasu gungun 'yan ta'adda sun kai hari cibiyar tsaron 'yan sanda na yankin Akila a yammacin Ajdabia dake gabashin kasar.

Majiyar ta ce 'yan ta'addar sun banakawa ofishin wuta, tare da kone duk wasu motoci da jami'an tsaron.

Tun a shekarar 2011 ne kasar Libiya ta fada cikin rikici biyo bayan goyon bayan da Amurka da kuma kungiyar tsaron Nato suka yiwa 'yan tawayen kasar wajen kifar da gwamnatin marigayyi kanal Mu'amar kaddafi.

Wannan lamari dai ya sanya kasar ta zamanto matattarar 'yan ta'adda daga kasashen daban daban na Duniya kafin daga bisani Sojojin kasar karkashin jagorancin janar Khalifa Haftar suka samu nasarar fatattakarsu daga mafi yawan yankunan da suka mamaye a baya.