An Hallaka 'Yan Ta'addar ISIS 13 A Gabashin Libiya
Majiyar tsaron kasar Libiya ta sanar da hallakar 'yan ta'adda ISIS 13 a yayin gumurzu da Sojoji a gabashin kasar
Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto majiyar tsaron Libiya na cewa Sojojin kasar sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addar ISIS 13 a yankin Akilah na garin Ajdabiya dake gabashin kasar.
Sanarwar ta ce mahmud Bar'asi kwamandar 'yan ta'addar ISIS din na daga cikin wadanda aka hallaka a yayin fafatawar tsakanin sojoji da 'yan ta'addar.
A ranar talatar da ta gabata ma 'yan ta'addar na ISIS sun kai hari Ofishin 'yan sanda na yankin Akilah dake garin Ajdabiya inda suka kashe jami'an 'yan sanda biyu da kuma jikkata wani na daban, inda suka banka wuta a cikin ofishin, lamarin da ya yi sanadiyar kone duk wasu motoci, makamai da kayen aikin 'yan sandar, sannan kuma suka shiga cikin gari suka kwashe kayayyakin abinci da sauransu a shaguna.
Libiya dai ta fada cikin rikici tun bayan da 'yan tawaye bisa goyon bayan Amurka da kungiyar tsaron Nato suka kifar da gwamnatin marigayyi Kanal Kaddafi a shekarar 2011.