An Kama 'Yan Ta'adda Da Dama A Tsakanin Iyakokin Aljeriya Da Tunisiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32509-an_kama_'yan_ta'adda_da_dama_a_tsakanin_iyakokin_aljeriya_da_tunisiya
Ma'aikatar tsaron Aljeriya ce ta sanar da kame 'yan ta'addar akan iyakarta da kasar Tunisiya
(last modified 2018-08-22T11:32:10+00:00 )
Jul 28, 2018 08:29 UTC
  • An Kama 'Yan Ta'adda Da Dama A Tsakanin Iyakokin Aljeriya Da Tunisiya

Ma'aikatar tsaron Aljeriya ce ta sanar da kame 'yan ta'addar akan iyakarta da kasar Tunisiya

Kamfanin dillancin labaran Fars ya ambato wani bayani da ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta fitar da a ciki ta ce; An Kame 'yan ta'adda 18 ne a  wani samame na hadin gwuiwa da jami'an tsaron kasar Tunisiya a gundumar Tebessa.

Sojojin kasar ta Aljeriya sun bude sintiri da kai farmaki akan iyaka da kasar Tunisiya tun bayan kisan da 'yan ta'adda su ka yi wa jami'an tsaron kasar Tunsiya kusan watanni biyu da su ka gabata.

Tun a 2014 ne dai kasashen Aljeriya da Tunisiya su ka kafa rundunar hadin gwuiwa domin fuskantar  matsalar ta'addanci da ta addabe su.