Mutanen Kasar Libya Sun Gudanar Da Zanga Zanga Ta Neman Kyautata Rayuwarsu
Mutanen kasar Libya a garuruwa daban daban sun gudanar da zanga zangar lumana a jiya jumma'a a garuruwan kasar da dama don neman gwamnatin kasar ta kyautata rayuwarsu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran an gudanar da zanga zangar a birnin Tripoli babban birnin kasar da kuma wasu garuruwa da dama. A karshen zanga zangar mutanen kasar ta Libya sun bukaci jami'an gwamnatin kasar su maida hankali wajen samar da bukatun mutanen kasar.
Har'ila yau masu zamga zangar sun bukaci a gudanar da zabubbuka a kasar kafin karshen wannan shekara don ita ce kadai hanyar maita kasar kan hanyar da ta da ce. Banda haka sun bukaci a samar da yansanda don dawo zaman lafiya a kasar don kuma hukunta wadanda suka kira barayin kudaden mutanen kasar.
Daga karshe masu zanga zangar sun kuduri anniyar gudanar da zanga zangar lumana a ko wace jumma'a har zuwa lokacinda aka biya bukatunsu.