An Sauke Ministan Tsaron Kasar Libya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32550-an_sauke_ministan_tsaron_kasar_libya
Shugaban gwamnatin hadin kan kasar ta Libya Fayez al-Siraj ne ya sanar da sauke al-Mahadi al-Barghathi daga kan mukaminsa na ministan tsaro.
(last modified 2018-08-22T11:32:10+00:00 )
Jul 30, 2018 12:14 UTC
  • An Sauke Ministan Tsaron Kasar Libya

Shugaban gwamnatin hadin kan kasar ta Libya Fayez al-Siraj ne ya sanar da sauke al-Mahadi al-Barghathi daga kan mukaminsa na ministan tsaro.

Shugaban gwamnatin hadin kan kasar ta Libya ya sanar da cewa an sauke ministan tsaron ne daga kan mukaminsa saboda yana da hannu a cikin harin da aka kai wa sansanin sojan sama na Brak da ke yankin Wadi al Shati da ke yammacin kasar a ranar 18 ga watan Mayu na 2017.

A yayin wancan harin dai an kashe mutane 150 tare da jikkata wasu daruruwa.

Libya ta fada cikin rashin tsaro ne tun 2011 bayan kisan da aka yi wa mu'ammar Khaddafi.