Ana Daukar Matakan Dakile Bullar Ebola A Congo
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sanar cewa ta aike da magunguna da kuma ma'aikatan kiwon lafiya zuwa yankunan da aka sami bullar ta Ebola a kasar ta Demokradiyyar Congo
Sake bullar cutar ta Ebola ya biyo bayan mako guda kacal da aka sanar da cewa an kawo karshenta a yankin Beni da ke gabacin kasar.
Watanni takwas da su ka gabata ne dai cutar ta bulla a garin Bikoro da ke gundumar Equateur a yankin arewa maso yammacin kasar, daga can kuma ta yadu zuwa garin Mbandaka da ke tsakiyar wannan gundumar.
A karshen shekarar 2013 ne wannan cuta ta bulla a kasashen yammacin Afirka ta kuma ci gaba da duakar rayukan mutane 11,000 da 300 har zuwa 2016.
Kasashen da cutar ta fi yin barna su ne Demokradiyyar Congo da Liberia, Gunea, da Saliyo.